Matakin na zuwa ne,a yayin da Kasar ta ce, ta samu nasarar shawo kan cutar Korona wadda masana kimiyya ke cewa ta samo asali daga can.
China zata sake dawo da bada bizar shiga cikin kasar ta ga baki masu sha’awar yawon bude ido ,tun bayan data rufe iyakokinta a sakamakon annobar sarkewar numfashi ta korona shekara ukku data gabata.
Sanarwar na zuwa ne bayan da kasar ta samu nasarar murkushe cutar ta Korona,bayan data dauki matakan kakkabe cutar tsawon shekaru ukku da suka wuce.
A jiya ne, Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen kasar China, Ji Rong,Ya tabbatar da cewar kasar zata dawo bayar da bizar shiga kasar ta ga ‘yan kasashen waje daga yau Laraba.
Kazalika sanarwar ta baiyana cewar bizar shiga kasar da aka bayar kafin ranar 28 ga watan Maris din 2020, amma kuma aka kulle kasar daga bisani, a halin yanzu zata yi aiki ga wadanda aka baiwa bizar tunda farko.