On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Yau Laraba Kungiyoyin Kwadago A Najeriya Ke Jagorantar Zanga-Zangar Adawa Da Tsadar Rayuwa

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC, ta yi watsi da matakin dakatar da duk wani tsari da haifar da karin farashin man fetur da sauran sauran matakan  gwamnatin tarayya da suka jefa talakawa cikin halin tsadar rayuwa, inda ta ce babu gudu babu ja da baya kan zanga-zangar da ta shirya yi a yau laraba 2 ga watan Agusta 2023.

 

Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan a daren da ya gabata a Abuja, sa’o’i bayan wata ganawa da wakilan gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Femi Gbajabiamila.

Shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo a baya ya ce shugabannin ƙwadago sun shiga wani zama don yanke shawara kan zanga-zangar kamar yadda Gbajabiamila yace akwai alamun ƙungiyar ba za ta cigaba da shirin zanga-zangar ba.

Sai dai a nasa jawabin, Ajaero ya umarci rassan kungiyar na jihohi  da su dauki matakin tabbatar da zanga-zangar, yana mai cewa ganawar da suka yi da gwamnatin tarayya bata sauya matsayar kungiyar ba.