A yaune kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kano zata yanke hukunci kan bukatar da jam’iyyar APC ta shigar gabanta inda take neman a bata damar duba Na’urar tantance masu zabe ta BVAS da aka yi amafani dasu a lokacin zaben gwamnan jihar Kano.
A yayin zaman kotun na jiya, Lauyan jam’iyyar APC Nuraini Jimoh SAN, Ya bukaci kotun data baiwa wadanda yake karewa damar duba na’urorin tantance masu zaben da hukumar zabe ta kasa ta yi amfani dasu a lokacin zaben.
Sai dai lauyan wadanda ake kara, Barrister E Osayomi ye nemi kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan kano da ta yi wancakali da bukatar da jam’iyayr ta APC ta shigar gabanta, inda ya ce lauyan bashi da hurumin shigar da bukatar a cikin kasa da kwanaki goma da rufe karbar bayanan kara.
Mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ya saka yau juma’a domin yanke hukunci akan bukatar, kazalika ya saka ranar litinin mai zuwa a matsayin rana ta karshe da za’a kammala zaman share fage na shari’ar, domin fara zaman karar gadan-gadan.