Dakataccen gwamnan Babban bankin kasa, Godwin Emefiele , Ya shiga rana ta shida ya na tsare a hannun hukumar tsaron farin kaya ta DSS, bisa zarginsa da daukar nauyin aikata lefukan ta’adanci, da kuma badakalar kudade.
Ana yin bincike kan dakataccen gwamnan bankin kasar ne ta cikin sirri, A yayin da yau yake shiga rana ta shida, tun bayan da jami’an tsaron farin kayan suka yi awon gaba da shi, ba tare da anji wani karin bayani ba.
Idan ba’a manta ba tunda farko alaka ta yi tsami tsakanin Hukumar tsaro ta farin kaya DSS da kuma dakataccen gwamnan babban bankin kasa,bisa zarginsa da aikata wasu lefuka , wanda koda a cikin watan Disambar bara, Hukumar ta nemi umarnin kotu ta cikin sirri domin cafke shi.
Babu dai wasu alamu dake nuni da cewar za’a iya sakin dakataccen gwamnan bankin kasar a nan kusa, Yayin da har yanzu hukumar tsaron bata kaiga yiwa jama’a bayani kan binciken da take gudanarwa a kansa.