On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Yau Alhamis Kotun Koli A Najeriya Ke Yanke Hukunci Kan Shari'ar Zaben Shugaban Kasa Na 2023

‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi, A yau ne za su san makomarsu yayin da kotun koli ke shirin yanke hukunci a karar da suka shigar ta kalubalantar  ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gabata a watan Maris na wannan shekara.

Sun kai jam’iyyar APC da dan takararta kara kotu bisa Ikirarin wasu wasu kura-kurai da dama

A ranar Laraba ne kotun da dukkan bangarorin da abin ya shafa suka tabbatar da ranar yanke hukuncin.