‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a ceto kasarnan daga gazawar shugabancin da ke ci gaba da dagula ci gabanta tsawon shekaru.
Da yake jawabi a taron shugabannin kasa da kasa na Jamie Pajoel a Owerri, Obi ya alakanta gazawar shugabanci a Najeriya da rashin ƙwararrun direbobi da ba su da lasisin tuka mota.
Ya ce irin wannan yanayi ba zai haifar da komai ba Illa tabarbarewar al’amura.
Ya bayyana cewa koma-bayan da ake gani a kusan kowane bangare ya samo asali ne saboda babu shugabanci na gaskiya a kasar nan.