On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Yanzu Lokaci Ne Da Sanatan Kudu Maso Kudu Zai Shugabanci Majalissar Dattawan Najeriya - PANDEF

Kungiyar Pan Neja Delta PANDEF ta bukaci shugabannin jam’iyyar APC da su zabi shugaban majalisar dattawa daga shiyyar Kudu maso Kudu don samar da daidaito da adalci.

A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Ken Robinson ya fitar, ya ce yana da muhimmanci  jam’iyya mai mulki wacce ke da mafi yawan zababbun Sanatoci, ta ware matsayin shugabancin majalissar Dattawa ga shiyyar Kudu-maso-Kudu.

Jam’iyyar APC ta lashe mafi yawan kujerun ‘yan majalisar dokoki a lokacin zabe da sama da kujeru 55 daga cikin kujeru 109 na majalisar Dattijai da sama da 160 daga cikin kujeru 360 na majalisar wakilai.

Ana sa ran jam’iyyar za ta fitar da tsarin karba-karba na shiyya-shiyya bayan kammala azumin watan Ramadan, kamar yadda kakakin majalisar dattawa, Ajibola Bashiru ya bayyana.