On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Yanzu A Jihar Borno Babu Wani Sauran Gari A Karkashin Ikon 'Yan Tada Kayar Baya - Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ce babu wani gari a jihar da har yanzu ke karkashin ikon 'yan ta'adda na Boko Haram.

Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Maiduguri lokacin da ya karbi bakuncin babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa da ya kai masa ziyara.

Ya yabawa sojoji bisa sadaukarwar da suka yi wajen dawo da zaman lafiya a Borno.

Gwamnan ya amince da rawar da Janar  Musa ya taka a matsayin kwamanda wajen maido da zaman lafiya a Borno kafin hawansa matsayin babban Hafsan sojoji.

Tun da farko, Janar Musa ya ce ya je Borno ne domin ya kara kwarin gwiwar sojojin da kuma godewa gwamnati da al’ummar Borno bisa goyon bayan da suka bayar.

Musa, wanda ya tuna zamansa a Borno a matsayin Kwamanda, ya ce ya samu goyon baya mafi yawa daga gwamna da kuma mutanen Borno.