Kwamishinan yansandan jihar Kano, Hussaini Gumel ya tabbatar da cafke wani Darakta a Ma’aikatar samar da albarkatun ruwan shat a jihar Kano, Mai suna Abubakar Gambo, tare da wasu mutane biyu saboda samunsu da lefin yin gwanjon wasu kayayyaki mallakin gwamnati
Kwamishinan ya fadawa manema labarai a jiya cewar, Sauran mutanen biyu sun hada da Baba Yahya wanda ya kasance mataimakin sakataren mulki sai kuma Nuhu Mansir wanda ya kasance tsohon mai kula da shirin noman rana na KAREFA a karamar hukumar Tudun Wada, wadanda suma tuni suka fada komar su.
Ya zarge su da yin satar saka hannu a cikin wata wasika dake halasta, yin gwanjon wasu manyan kayayyaki na fanfunan samar da ruwa da kuma Tankokin ajiyar ruwa, wadanda kwamishinan ruwa na jihar Kano, Ali Haruna Makoda, ya musanta bada izinin yin gwanjon kayayyakin.
Kwamishinan yansandan jihar kano, ya ce za’a mika batun gaban kotu, da zarar sun kammala bincike.