Rahotanni sun daruruwan mayakan Boko Haram da iyalansu sun bar sansanoninsu, sakamakon ambaliyar ruwa da ta yi barna a yankunansu, al’amarin da ya tilasta musu yin kaura zuwa wasu wuraren da ba a amince da su ba a gefen dajin Sambisa.
An rawaito cewa ambaliya da kogin Yedzaram ya yi ta shafi sansanonin ‘yan ta’adda da dama a Sheuri da mazabar Kumshe da Gaizuwa a ranar Lahadi.
Idan ba a manta ba a jiya mun bayar da rahoton yadda ‘yan tada kayar baya 70 suka nutse a ruwa bayan dakarun soji sun hallaka sama da mutum 200 daga cikinsu da suka hada da kwamandoji biyar biyo bayan hari ta sama a karshen mako.
Baya ga amabaliyar kuma, karancin makamai, da abinci ma na daga dalilan tserewar ta su.
A hannu guda kuma, wani Kwamnadan kungiyar Goni Farooq ya mika wuya ga rundunar soji a Karamar Hukumar Bama da ke Jihar Borno a ranar Lahadi.
Wata majiyar sirri ta bayyana cewa Kwamnadan ya kuma mika makamai da suka hada da AK47 45, da harsasai, da manyan bindigogi, da na`urar samar da lantarki mai amfani da hasken rana, da sutura da sauran kayayyaki.