Rahotanni na baiyana cewa an halaka wasu wasu sojoji yayin da Mayakan Boko Haram suka kai farmaki wani shingen binciken dakarun sojoji da ke kusa da dutsen Zuma a jihar Neja, a daren jiya.
Wajen da abun ya faru wanda yake kusa da garin Madalla bashi da wani nisa daga Zuba dake kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Wasu ganau ba jiyau ba sun fadawa manema Labarai cewa maharan sun isa wurin ne bayan karfe 7 na dare, inda nan take suka bude wuta.
Sun kara da cewa ‘yan ta’addar sun kwace ikon yankin na kusan mintuna 30 sannan suka ci gaba da harbe-harbe babu kakkautawa kafin daga bisani su tunkari babbar hanyar zuwa Kaduna
Sai dai kuma daga bisani tawagar jami’an yansanda masu aikin sintiri su isa wurin da abun ya faru.