Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare hallaka jami’in hukumar shige da fice ta kasa, da kuma jikata wasu jami’ai biyu a jihar Jigawa.
Kwanturolan hukumar a jihar Jigawa Ismail Abba shine ya tabbatar da hakan da yammacin jiya Laraba a wani taron manema labarai a Dutse babban birnin jihar.
A cewar Abba, ‘yan bindigar sun yi galaba akan jami’an ne, bayan wani hari da suka kai a sansanin jami’an na kula da shige da fice dake sintiri a Birniwa zuwa Galadi a daren ranar Talata.
Yace ‘Yan bindigan sun isa sansanin ne a kan babura biyu. Daya yana dauke da mutane uku, daya kuma na dauke da mutane biyu wanda daga isar su suka budewa ma’aikatan wuta, al’amarin da ya yi sanadin mutuwar daya daga cikinsu mai suna Abdullahi Mohammed, sannan wasu biyu daga cikinsu da suka hada da Abba Musa Kiyawa da Zubairu Garba suka raunata.
Sai dai sakamakon musayar wuta da ‘yan bindigar suka yi da jami’an, sun tsere cikin daji inda suka yi watsi da babura da wayar hannu kirara Tecno.
Kwantrolan yace tuni akayi jana’aizar jami’in da ya mutu jiya laraba bayan karfe 2 na rana a birnin dutse yayinda jami’an biyu ke Asibiti karkashin kulawar likitoci.