Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da kama mutanen a wata zantawa da manema labarai a Damaturu.
Ya ce mutanen biyu sun yi ikirarin cewa su sojoji ne da ke aiki da bataliya ta 241 a Nguru, inda ya kara da cewa al’amarin ya faru ne da karfe 10 na daren ranar Juma’a bayan da Aisami ya ragewa daya daga cikin wadanda ake zargin hanya.
Ya bayyana cewa Aisami yana tuka motarsa zuwa Gashua daga Nguru, sai babban wanda ake zargin dake sanye da kayan sojoji ya roke shi da ya rage ma sa hanya zuwa Jaji-Maji.