On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

'Yan Sanda Sun Kama Mutane 6 Da Suka Nuna Rashin Da'a Ga Mai Martaba Sarkin Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane shida da ake zargi da rera kalaman batanci ga maimartaba  Sarkin Kano yayin bikin kaddamar da asibitin yara na Hasiya Bayero ranar Lahadi.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, ya ce wadanda ake zargin suna rera taken “Sabon Gwamna, sabon sarki.

Gumel ya kara da cewa, ‘yan sanda sun yi amfani da fasaha wajen zakulo wadanda ke da hannu a al’amarin, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo wadanda ake zargi da daukar nauyinsu.