Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Benue ta kama wasu mutum 18 da ake zargi da satar mutane a sassan jihar
Mai magana da yawun rundunar, Catherine Anene Sewuese, itace ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar litinin, tace mutanen da ake zargi sun yi kokarin tserewa jami'an 'yan sanda a wani wajen binciken ababen hawa a karamar hukumar Utonkon inda aka kama su.
Ta ce an samu makamai a wajen mutanen ciki har da bindiga daya samfurin AK-47, da kananan bindigogi biyu da kuma alburusai da dama da aka nade a jarida.
Mai magana da yawun 'yan sandan ta ce tuni aka kaddamar da bincike a kan mutanen wadanda yanzu haka ke hannun 'yan sanda a tsare.