Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman ga Gwamna Abba Yusuf da wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin karkatar da kayan abinci.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Hussaini Gumel, ya tabbatarwa manema labarai hakan a karshen mako, an kama wadanda ake zargin ne a wani wurin ajiyar kayayyaki da ke rukunin masana’antu naSharada dauke da buhuna sama da 200 da babu komai a ciki da suke amfani da su wajen sauya mazubin shinkafa da masara.
Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike na gaskiya.