Rundunar yansandan jihar Kano ta cafke wata Bazawara mai suna Rahma Sulaiman ‘yar shekara 25 a duniya, bisa zargin da ake mata na yin garkuwa da ‘yarta mai kimanin shekara 6 a duniya, mai suna Hafsat Kabiru tare da neman kudin fansa har naira milyan 3 daga hannun tsohon mijinta Kabiru Shehu,wanda ya kasance mahaifin yarinyar.
Kwamishinan yansandan jihar Kano, CP Usaini Muhammad Gumel ya fadawa manema labarai cewar, rundunar ta samu labarin faruwar al’amarin ne daga Kabiru shehu a ranar 8 ga watan Mayun da muke ciki.
Kabiru Shehu ya fadawa rundunar ‘yanansandan jihar Kano cewar, Tsohuwar matar tasa Rahma, ta gaya masa cewar yarinyarsa Hafsat Kabiru ta bace, Kuma wasu mutane sun kira ta suna neman a basu naira milyan 3 a matsayin kudin fansa.
Kwamishinan yansandan jihar Kano, Ya ce an samu nasarar kubutar da yarinyar a karamar hukumar Madobi dake nan jihar kano, yayin da kuma aka cafke mahaifiyar tata, inda daga bisani ta tabbatar da aikata lefin.
Wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya, ya ruwaito mana cewar rundunar ‘yansandan jihar Kanon, ta kuma samu nasarar kama daurin tabar wiwi har guda 605 da sauran miyagun kwayoyi daga hannun wasu mutane da ake zargi da dillancin miyagun kwayoyi, inda yanzu haka ake cigaba da bincike.