An kuma garzaya da wasu 'yan sanda biyu da suka ji raunuka a hadarin zuwa Asibiti
Ayarin motocin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sun yi hatsari a Abuja al'amarin da yayi sanadiyar mutuwar wasu ‘yan sanda biyu da suke aiki tare da tsohon shugaban.
Da yammacin ranar Laraba ne hadarin ya faru lokacin da Jonathan ya bar filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe domin zuwa gidansa da ke Abuja.
A watan sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban kasar Ikechukwu Eze ya fitar, yace Jonathan ya nuna matukar bakin cikinsa kan mutuwar 'yan sandan.
An kuma garzaya da wasu 'yan sanda biyu da suka ji raunuka a hadarin zuwa Asibiti .
Eze yace hatsarin bai shafi tsohon shugaban kasar ba, saboda motar da ke dauke da 'yan sandan ce ta kauce hanya a lokacin da direban ya rasa yadda zai yi, al’amarin da ya yi sanadin mutuwar 'yan sandan biyu.
Bayanai Jonathan ya tsira ba tare da kwarzane be, inda yayi Addu’a ga mamatan ‘yan sandan tare da mika ta’aziyya ga Iyalansu da kasa baki daya.