Rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa ta tabbatar da sace daliban Jami’ar Jihar ta Nasarawa da ke Keffi a daren ranar Litinin a unguwar Ka’are da ke garin na Keffi.
A baya wata majiya ta shaidawa jaridar dailytrust cewa wadanda abin ya shafa sun hadar da Rahila Hanya da Josephine Gershon da Rosemary Samuel da Goodness Samuel.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Ramhan Nansel, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce kokarin ceto daliban bai yi nasara ba.
Sai dai ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Maiyaki Baba, ya bayar da umarnin a farauto masu laifin da nufin ceto wadanda al’amarin ya rutsa da su.