‘Yan Najeriya za su fuskanci karin farashin abubuwan sha yayin da Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da harajin Naira 10 akan kowace lita ta abubuwan sha.
A cewar babban jami’in hukumar kwastam, sashen haraji, da shirin ciniki bai daya da kuma karfafa masana’antu, Dennis Ituma, harajin zai taimaka wajen yaki da cututtuka masu yaduwa.
Ya ce an fara aiwatar da harajin na Naira 10 ga kowace lita na kayan sha masu zaki a ranar 1 ga watan Yuni kuma zuwa ranar 21 ga watan Yuli, dole ne a tattara dukkan kudaden harajin da aka biya a asusun tarayya.
Ituma ya kara da cewa haraji wata manufa ce ta Gwamnatin Tarayya a shekarun Alif dari 9 da 84 amma an dakatar da tsarin a watan Janairun 2009 lokacin da aka cire abubuwan sha daga cikin masu biyan haraji.