Yawan kudin da jama’ar kasar nan suka kashe a bangare kiran waya da kuma siyan Data ya karu da kimanin naira Tiriliyan 2 da bilyan 59 a cikin watanni 9n farko na shekarar da muke ciki.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kanfanonin sadarwa na MTN Nigeria da Airtel Africa suka fitar.
Hakan ya nuna cewar an samu karuwar kaso 32 da digo 57 cikin 100 daga adadin kudin da aka kashe a irin wannan tsuki na shekarar bara, wanda ya kama naira tiriliyan 1 da bilyan 95.
Yawan karuwar kudin da ake kashewa wajen kiran waya da kuma na Data nada alaka da yadda aka samu karuwar masu amfani da Data da kuma karyewar darajar Naira.