Wani rahoton hadin gwiwa da shirin bunkasa samar da Abinci na Duniya da kuma Hukumar samar da Abinci da bunkasa aikin gona ta Majalisar dinkin duniya suka fitar, ya ce sama da ‘yan Najeriya miliyan 24 da dubu dari 8 na fuskantar barazanar karancin abinci tsakanin watan Yuni da Agusta.
Rahoton wanda aka wallafa shi a ranar Litinin ya bayyana kasashen Najeriya da Afghanistan da Sudan ta Kudu a cikin kasashe 18 da ke fama da yunwa a duniya.
Rahoton ya ce dukkan wuraren da aka zaiyana suna da tarin jama’a dake cikin matsalar rashin abinci, ko kuma suke fuskantar samun matsalar.
Rahoton ya ce, ana sa ran za’a iya fuskantar karuwar matsalar karancin rashin abinci a Najeriya nan gaba, sakamakon matsalar tsaro da ake fama da ita, tare da raunin tattalin arziki da kuma kalubalen sauyin yanayi.