Mutane milyan daya da dubu dari takwas ne suka amfana da shirye-shiryen.
Gwamnatin tarayya ta ce mutane miliyan 1 da dubu dari 8 ne suka ci gajiyar ayyuka da shirye-shiryen da aka yi a karkashin shirin rage talauci na kasa tare da dabarun bunkasa cigaban kasa.
A jiya ne aka gabatar da rahoton yadda aka gudanar da shirye shiryen a Abuja a yayin wani taro da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Rahoton ya ce, an yi shirye-shirye har guda 100 karkashin shirin bunkasa noma domin samar da abinci da ayyukan yi da kuma gina hanyoyin karkara.
Kakakin mataimakin shugaban kasa Laolu Akande, ya ce rahoton ya nuna cewa kananan manoma miliyan 1 da dubu dari 6 ne suka amfana da tsare tsaren da gwamnatin ta aiwatar.