Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa, Ta ce sama da mutane Dubu 40 ne ke mutuwa a Najeriya a duk shekara, sakamakon hadurran ababen hawa daban daban a kasar nan.
Wani babban jami’i a hukumar, Dauda Biu ne ya bayyana haka jiya a Abuja, yayin gudanar da bukukuwan makon kare afkuwar hadurra na Majalisar Dinkin Duniya karo na 7.
Ya kuma ce mutane miliyan 1 da dubu dari 3 ne ake kashewa ke mutuwa a kowace shekara a fadin duniya, sakamakon afkuwar hadurra.
A cewarsa, Babbar barazanar dake tattare da hadarin tafi ritsawa da mutane dake tsakanin shekara 5 zuwa 29 .