‘Yan Najeriya da dama sun shiga cikin halin kunci da yunwa da kuma rashin aikin yi a kasar Burtaniya, bayan da suka biya makudan kudi ga kanfanonin dake shirya tafiye tafiye, domin barin kasar nan , don samun aiyuka masu gwabi a kasar.
Kamar yadda kafar yada labarai ta Sky News ta ruwaito, Ta baiyana cewar, ‘yan Najeriyar da suka baiyana halin da suke a ciki, sun ce sun biya ma’aikatan kanfanonin kudi,domin samar masu da bizar yin aiki a kasar, amma da suka isa Ingilar sai suka fahimci babu wuraren aiyukan.
Daya daga cikin mutane, Ta baiyana cewar a halin yanzu guzurinta ya ‘kare duk da cewar anyi mata alkawarin samun aiki.
Kazalika itama wata mata ta ce sai da ta biya Fam dubu 10 domin kaita kasar ta Burtaniya da zummar samun aiki, amma Sabanin haka, Da isar kasar ke da wuya, Ta fahimci cewar babu aikin da take nema.