Rahotanni na baiyana cewa wasu ‘yan Najeriya na yin kaura zuwa kasashen waje yayin da adadin fasfo din da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ke bayarwa ya karu da kashi 38 cikin 100 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021.
Binciken ya nuna cewa hukumar ta bayar da fasfo dubu 767 da 164 a shekarar 2020, amma a shekarar 2021 sai da ta bayar da fasfo milyan 1 da dubu 59 da 607.
Bayanan da aka samu daga hukumar ta NIS, sun nuna cewa, daga cikin adadadin da aka bayar, fasfo 444 kadai suka kasance na jami’an gwamnati.
Har ila yau, wani bincike na Bankin Duniya ya nuna cewa ‘yan Najeriya dubu 56,000 ne ke barin kasar nan a duk shekara.