Shugaban ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, David Greene, ya ce, ofishin jakadancin ya tantance 'yan Najeriya sama da dubu 150 dake neman bizar Amurka, baya ga masu neman bizar dalibai su dubu 30.
Greene, wanda ya bayyana hakan a wata zantawa da Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya a Abuja, ya ce offishin na ci gaba da jajircewa wajen magance duk wasu matsalolin da suka shafi biza.
Ya bukaci masu sha'awar tafiya zuwa Amurka da su nemi wuri da akan lokaci kuma su tabbatar da cewa buƙatun biza sunbi tsare-tsaren da suka kamata.