On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Yan Majalissar Dokoki A Najeriya Sun Maida Martani Ga Masu Sukar Shirin Sayen Motocin Alfarma

Duk da kurar da ta taso a cikin ‘yan kwanakin nan, majalisar dattawan na bayar da hujja da kare matakinta na  shirin sayen motocin alfarma akan  Naira miliyan 160 kowacce Mota.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a Abuja, Shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa, Sunday Karimi, ya ce shugabannin majalisun biyu sun yanke shawarar sayen motocin alfarma ga ‘yan majalisar ne saboda dorewa da kula da su na tsawon shekaru hudu.

Karimi ya ci gaba da cewa ‘yan Najeriya na sa ido akan  ‘yan majalisa amma sun manta da ministoci domin a cewarsa wasu ministocin suna da motocin alfarma sama da uku kuma ba a tuhumarsu.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki bayan da jama’a suka yi ta cece-kuce kan yadda ‘yan majalisar za su sayi motoci wanda farashinsu ya kai naira miliyan 160 kowacce.