Majalisar Wakilai ta fara wani sabon yunkuri na tsawaita amfani da sakamakon jarrabawar neman gurbin shiga Jami’oi UTME.
Hakan ya biyo bayan wani kudiri da Akintunde Rotimi na jam’iyyar APC daga Legas ya gabatar, inda ya ce ya kamata JAMB ta tsawaita wa’adin aiki da sakamakon jarabawar UTME daga shekara daya zuwa shekaru uku tare da gudanar da jarrabawar sau biyu a shekara.
A majalisa ta tara, ‘yar majalissa Tolulope Shadipe ta jam’iyyar APC daga jihar Oyo ta dauki nauyin kudirin dokar tsawaita amfani da sakamakon jarabawar UTME tsawon shekaru hudu, amma ba a amince da bukatar ba kafin majalisar tazo karshe..
Yayin da kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya bada damar kada kuri’a a jiya, ‘yan majalisar sun amince da kudurin baki daya, inda suka bukaci ma’aikatar ilimi ta tarayya da ta tabbatar da cewa an aiwatar da kudurin.