On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

'Yan Majalissar Dokoki A Jihar Kano Sun Karrama 'Dan Adaidaitasahu Da Naira Milliyan 1.5

Zauren majalissar dokokin Jihar Kano

Majalisar dokokin jihar Kano a zamanta na yau ta karrama tare da bayar da gudunmawar Naira miliyan 1.5 ga Auwalu Salisu wanda ake kira 'DanBaba wani mai tukin Baburin Adaidaitasahu da ya mayar da kudin da aka manta a baburinsa ta hannun Arewa Radio Kano.

Idan za a iya tunawa, a ranar 18 ga Satumba na  2023 ‘yan majalisar dokokin Kano guda 40 sun yi alkawarin bayar da wani  kaso daga cikin albashinsu, ga matashin mai shekaru 22  da ya mayar da kudin sama da  miliyan 15 ga wani dan kasar Chadi a Kano, domin nuna jin dadinsu kan gaskiya da nagartar da ya nuna. 

Yayin gabatar da takardar shaidar yabo da tsabar kudi da ‘yan majalisar suka bayar, kakakin majalisar Hon Isma’il Jibril Falgore, ya ce Auwalu ya tabbatar da nagarta   ta hanyar mayar da kudaden da aka manta, duk kuwa da halin da iyayensa ke ciki, da kuma halin matsin tattalin arziki  a Najeriya. 

A wata zantawa da aka yi da shi bayan karbar gudunmawar, matashi ‘DanBaba wanda ya samu rakiyar manajan Arewa Radio Shehu Bala Muhammad Kabara, ya nuna jin dadinsa ga ‘yan majalisar da suka karrama shi wanda ya ce ba zai manta da su ba, ya kuma yi addu’ar samun nasara ga zauren majalisar.