‘Yan majalisar dokokin jihar Filato 16 da Kotun daukaka kara ta sauke daga kan kujerunsu a watan Nuwambar shekarar data gabata, sun lashi takobin shiga zauren majalisar dokokin jihar a yau, domin cigaba da gudanar da aiyukansu, kamar yadda suka baiyanawa manema Labarai a jiya.
Idan ba’a manta ba, Kotun daukaka kara ta soke zaben ‘yan majalisun 16 na jam’iyyar PDP saboda rashin yin aiki da tsarin da jam’iyya ta shimfida wajen fitar da ‘yan takara. Haka zalika kotun daukaka karar ta soke zaben wasu ‘yan majalisun dokokin tarayya da kuma na gwamnan jihar Caleb Mutfwang.
To sai dai Kotun koli ta jingine hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke akan kujerar gwamnan jihar a ranar 12 ga watan da muke ciki, wanda ta nuna cewar kotun baya ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke.
Bayan sanar da hukuncin kotun kolin ne, Yan majalisar ta bakin mai magana da yawunsu, Ishaku Maren, suka yi ikirarin cewar hutu kawai suka je, kuma yau zasu koma bakin aiki.