On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Yan Kasar Ecouador Sun Zabi Matashi A Matsayin Shugaban Kasa

Daniel Noboa, mai shekaru 35, ya zama zababben shugaban kasar Ecuador mafi karancin shekaru a ranar Lahadin data gabata.

Koda  aka kirga kashi 90 cikin 100 na kuri'un da aka kada, hukumar zaben ta sanar da Noboa a matsayin wanda ya yi nasara.

A yanzu haka abokiyar hamayyarsa Yar jam'iyyar gurguzu, Luisa Gonzalez ta amince da shan kaye kuma ta taya mister Noboa murna.

Ta shaida wa manema labarai cewa ba za ta ce anyi magudin a zaben ba.

'Yan Ecuador sun kada kuri'a na tsawon sa'o'i 10 a ranar Lahadin da ta gabata ba tare da samun rahoton tashin hankali a kasar da ke fama da yakin muggan kwayoyi da kuma kashe-kashen siyasa, Wanda ya yi sanadin mutuwar  wani fitaccen dan takarar Shugaban Kasa, Fernando Villavicencio.