Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani ma’aikacin Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke karamar Hukumar Nasarawa Eggon a Jihar Nasarawa, Auta Nasela.
Al’amarin ya faru ne da karfe 8:45 na dare a karshen mako inda ‘yan bindigar suka farwa harabar makarantar inda suka je gidan marigayin domin neman kudi.
Rahotanni sunce Nasela ya gudu zuwa wani gidan makwabcinsa, inda maharani suka harbe shi har sai da ya mutu. Shi ma wani ma’aikacin makarantar, Timothy Malle, an harbe shi, amma ya tsira daga harin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce al’amarin harin ‘yan fashi da makami ne.