Kungiyar masu hada-hadar Chanjin kudaden waje a Jihar Kano ta bayyana damuwa akan yadda mambobinta suka yi asarar sama da Naira milliyan 278 a hannun ‘yan damfara a cikin makonni uku da suka gabata saboda rashin bin ka’idar sanin abokan hulda da sauran tanadin tsarin tafiyar da harkokin kudi na kasa.
Shugaban kwamitin sulhu na kungiyar Mansur Sama’ila ne ya bayyana haka a lokacin da tawagar hukumar EFCC ta kai ziyarar wayar da kan 'yan Kungiyar kan ka'idojin hada-hadar kudi da kuma rashin bin dokoki.
Ya ce wasu 'yan Chanji na fadawa hannun ‘yan damfara wadanda ke amfani da sabbin kananan bankuna da bankunan yanar gizo wajen hada-hadar kudi, yayinda matsalolin ke karuwa ba tare da samun kafofin bibiyar kudaden ba.
Da yake jawabi tun da farko, Barista Sadik Husaini daga sashen shari’a na hukumar EFCC shiyyar Kano, ya gargadi masu gudanar da canji da su nemi sanin ayyukan hukumar da sauran tsare-tsare na hada-hadar kudi a Najeriya, domin rashin sanin doka ba zai taba zama uzuri ba.Insert...
Shugaban Kungiyar Sani Salisu Dada, ya yi alkawarin cigaba da Nemo hanyoyi da matakan wayar da kan 'yan Kasuwar domin magance matsalolin da kuma samun cigaba.