On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mutum 6 A Jihar Edo

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane shida da suka hada da ‘yan wasa da jami’an kungiyar mata ta kasa a Uronigbe da ke kan iyaka tsakanin jihohin Edo da Delta a karamar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo.

Wakilinmu ya samu labarin cewa an yi garkuwa da mutanen shidan ne da  karfe 6 na yammacin ranar Juma’a, yayin da suke dawowa daga wani wasa a Owa-Alero da ke karamar hukumar Ika ta Arewa-maso-gabas a jihar Delta.

Wata majiya a yankin ta ce masu garkuwar sun tuntubi wasu iyalan mutanen inda suka bukaci a biya su kudin fansa Naira milliyan 5 kowannen su.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da sace mutanen, inda ya kara da cewa al’amarin ya faru ne a jihar Edo.