‘Yan bindiga sun halaka 2 daga cikin ‘yan sintiri yayinda suka yi awon gaba da wasu ma’aurata da kuma mazauna yankin Shola, a birnin jihar Katsina.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da karfe 1 da mintuna 25 n dare, inda suka shafe sa’o’I 4 tare da yin awon gaba da wasu daga cikin mazauna yankin.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa ‘yan kungiyar sintirin, su mayar da martani ga ‘yan bindigar, inda a nan ne suka halaka 2 daga cikin su, tare da raunata wasu.
Wani makusancin ma’auratan da aka yi garkuwar da su, Usman Masanawa, yace lokacin da maharan suka je yankin Angon Yusuf Bishir, ya kira shi domin ya shaida masa, amma hakan bai yiwu ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isa, ya bada tabbacin zai sanar da halin da ake ciki ga manema labarai a nan gaba.