Ukku daga cikin ragowar daliban nan Mata guda bakwai na makarantar ‘Yan Mata ta Birnin Yawuri a jihar Kebbi da suka rage tsare a hannun ‘yan bindiga sun shaki Iskar ‘Yanci.
Shugaban kungiyar Iyayen yaran da aka sace, Malam Salim Kaoje ya tabbatar da cewar, ‘Yan matan da aka saki sun isa birnin Kebbi da yammacin ranar Litinin.
Malam Salim ya ce sun biya wasu makudan kudi domin sakin hudu daga cikin daliban mata dake tsare a hannun ‘yan bindigar bayan sun sayar da wasu kadarorinsu, tare da gudunmuwar da suka samu daga wasu ‘Yan Najeriya da dama domin ganin an saki yaran.
Idan ba’a manta,’Yan Bindiga sunyi awon gaba da Dalibai mata 96 na makarantar Birnin Yawuri dake jihar Kebbi, a yayin wani hari da suka kai ranar 17 ga watan yunin 2021, yayin da koda a watan da ya gabata sai da aka saki hudu daga cikinsu.