A yankin Kudu-maso-gabas, wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari a wani ofishin hukumar zabe mai zaman kanta a karamar hukumar Oru ta Yamma a jihar Imo a ranar Lahadi.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe Festus Okoye shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
A ranar 1 ga watan Disamba da muke ciki an kai hari ofishin INEC a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.
Okoye ya ce harin ya shafi dakin taron ne, inda aka lalata kayayyakin ofishin da kayan aiki.
Sai dai duk da haka harin bai shafi sauran wurare masu mahimmanci ba.
Ya kara da cewa wannan shi ne hari na 7 da aka kai wa cibiyoyin INEC a jihohi biyar na tarayya cikin watanni hudu da suka gabata.
A wani bangaren kuwa, rundunar ‘yan sanda a jihar imo ta ce wasu ‘yan bindiga da ake zargin mambobin haramtacciyar kungiyar rajin kafa kasar Biafra ne masu dauke da makamai, sune suka kai hari offishin INEC a Jihar.
Ana dai zargin kungiyar da kai hari a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na karamar hukumar Oru ta kudu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mike Abattam, ya tabbatar da hakan a garin owerri a ranar Lahadin da ta gabata cewa.
Yace jami’an da ke bakin aiki, sun dakile harin.
Ya ce ‘yan bindigar sun jefa bama-bamai ne a ofishin daga wajen takatangar.
Haka kuma, ya ce yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, ana kokarin kamo wadanda ake zargi domin hukunta su.