Yan bindiga suka yi dirar mikiya fadar Basaraken Oghara dake karamar hukumar Kabba Bunu a jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da basaraken yankin.
Kazalika maharan sun tafi da wasu manyan hadiman basaraken wadanda suka hada David Obadofin da kuma wani mai suna Temidayo Elewa, a lokacin da suka kai harin.
Bugu da kari maharan sun bindige wata ‘yar aikin gida da suka tarar a fadar sarkin mai suna Toyin Onare.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, SP William Aya,Ya ce ‘yan bindigar sun farwa fadar basaraken ne da karfe ukku na dare,inda suka fara yin harbi a sama, kafin su kaiga kutsawa cikin fadar sarkin.
Ya kara da cewar a yanzu haka kwamishinan yansandan jihar Hakeem Yusuf ya tura tawagar jami’an yansanda ta musamman zuwa yankin da abun ya faru, domin kubutar da mutanen.