On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Yan Bindiga Sun Kashe Dagaci Tare Da Yin Garkuwa Da Mutane A Wani Sabon Hari A Jihar Neja

Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan bindiga sun kashe dagacin  kauyen Zazzaga da ke karamar hukumar Munya a Jihar Neja, Malam Usman Sarki, tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Wani shugaban al’ummar yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai a Munya cewa, ‘yan bindigar sun kaddamar da harin a garin Zazzaga da makwabta, a daren ranar Talata.

Majiyar ta ce an kuma yi garkuwa da wasu manoma da ba a tantance adadinsu ba da suka hada da mata.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai Abiodun ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan harin ba.