Wasu ‘yan ta’adda dauke da manyan bindigogi sun kai hari a majami’ar New Life dake karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da akalla mutane 25.
A cewar shaidun gani da ido, ‘yan ta’addan da ke kan babura sun mamaye cocin da ke unguwar Dan-Tsauni Gidan Haruna a safiyar Lahadi a lokacin da masu bauta ke cikin cocin.
Babban mataimaki na musamman ga Gwamna Aminu Masari kan harkokin mabiya Addinin Kirista, Ishaya Jurau ya tabbatarwa manema labarai.
Yace a halin yanzu jami’an tsaro sun bazama kuma suna bakin kokarinsu wajen ganin an ceto duk wadanda al’amarin ya rutsa da su.