Wasu ‘Yan bindiga da ba’a san ku su waye ba sun halaka mutane 38, wanda ya hada da kananan yara da kuma Mata a garin Taka Lafiya na karamar hukumar Karu, dake jihar Nasarawa.
Shaidun gani da ido sun fadawa jaridar daily trust cewar, al’amarin ya samo usuli ne makwanni biyu da suka gabata, Lokacin da wani Manomi dake a yankin Gwanja kusa da garin nasu na Taka lafiya, Ya tuhumi wani makiyayi saboda kyale shanunsa su shiga cikin gonarsa da ya yi sabuwar shuka a cikinta.
A ranar Alhamis din data gabata ce, ‘yan bindigar suka kaddamar da harin inda suka halaka mutane hudu a nan take, Sannan kuma ranar juma’a aka sake kawo Gawar mutane Bakwai daga garin na Takalafiya da sauran wasu garuruwa, Inda aka kaisu wurin ajiyar gawa na cibiyar Lafiya ta taraiyya dake birnin Keffi, yayin da har yanzu ba’a ga mutanen yankin da dama ba.
A ranar Asabar ne aka yi jana’izar mutane 38 da ‘yan bindigar suka halaka a garuruwan biyu, Mataimakin gwamnan jihar, Dr Emmanuel Akabe wanda ya jagoranci tawagar jami’an gwamnati, wajen binne mamatan, yayi tir da kisan gillar da aka yiwa mutanen.
Kazalikaya bada tabbacin cewar gwamnati zata bada tallafi ga wadanda aka raba da muhallansu,Sannan kuma ya bukace su dasu temakawa hukumomi da bayanan da suka dace.