Yan bindiga sun halaka wasu jami’an sintiri guda tara da aka fi sani da Yan Ba Beli a jihar Bauchi.
Lamarin ya faru ne a kauyen Gamji lokacin da jami’an sintirin ke farautar ‘yan bindigar da suka addabi garuruwan Karamar hukumar Ningi.
Rahotanni sun baiyana cewar yan bindigar sun yiwa jami’an sintirin kwantan bauna tare da halaka guda tara daga cikinsu a nan take, yayin da wasu kuma suka ji ciwuka.
Daya daga cikin ‘yan kungiyar sintirin da ya bukaci a sakaye sunansa, ya fadawa manema Labarai cewar lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadin data gabata a lokacin Jami’an Sintirin ke shiga tsaunikan dake kauyen Gamji domin neman yan bindigar.