Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a jihar Imo, inda suka yi awon gaba da wasu ‘yan jam’iyyar APC mai mulki biyu tare da kashe wasu mutum uku.
Bayanai sunce ‘yan bindigar sun kwace sashin Amaraku-Orji na sabuwar hanyar Owerri zuwa Okigwe da aka gyara inda suka shafe sa’o’i da dama.
Direban daya daga cikin wadanda akayi garkuwa da su na daga cikin wadanda aka kashe.
Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.