On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Yakubu Dogara Na Zargin Wasu ‘Yan Sanda Da Yunkurin Hallaka Shi

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, ya shigar da karar wasu ‘yan sanda gaban Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda kasarnan Usman Alkali Baba, bisa zargin yunkurin hallakashi shi.

A cikin karar da Dogara ya sanya wa hannu, dan majalisar ya yi zargin cewa wasu ‘yan sandan da aka bayyana sunayensu da Sufeto Dakat Samuel da Insfekta Auwalu Mohammed suna hada baki da wani Barau Joel Amos (Sarkin Yaki) wajen kulla makircin kashi shi.

Dogara ya ce ko da yake yanzu maganar na gaban mataimakin kwamishinan ‘yan sandan sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi,amma ya bukaci babban sufeton ‘yan sandan kasar ya kwan da  sanin haka.

Cikin wasikan da ya rubuta, tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya, Ya ce, ya tabbata cewa Usman Baba Alkali na sane da wannan lamari tun da al’amari ne da ya shafi wawashe runbun adana makaman ‘yan sanda  da ke Bauchi, wanda jami’an da aka ba su amanar tsare su, inda Barau Joel Amos, ya nemi ya sayansu, ko kuma ya kasance yana sayen bindigogi daga jami'an.