On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Yakin Israila Da Hamas Na Barazanar Haifar Da Yakin Duniya Na 3 - Majalissar Dattijan Najeriya

Majalisar dattawa ta bukataci  gwamnatin taraya ta hada hannu da sauran kasashen duniya domin kiran a tsagaita wuta a rikicin Israila da kuma Hamas.

Sunce rikicin yana tunawa da yakin basasan da akayi a Najeriya da kuma irin tashin hankalin da yan Najeriya suka fuskanta sakamakon yakin, inda majalisar ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta sake yin duba akan tsarin samar da kasa biyu a yankin domin magance matsalar rikicin Israila da Palastinu.

A wani kudiri da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaaila daga Kano ya tsara, aka kuma gabatar da shi jiya Talata a gaban majalisar bayan zazzafar muhawara, yanzu dai baki ya haɗu wajen neman Najeriya ta bayyana matsayarta a rikicin na Gaza.

Majalisar Dattawar ta bayyana mace-mace da kuma adadin waɗanda suka rasa muhallansu sakamakon rikicin na Isra'ila da Hamas a matsayin abin tsoro.

A tattaunawarsa da BBC Sanata Kawu Sumaila ya ce sun yi la'akari da abubuwan da suke faruwa sun kai maƙura da ya kamata Najeriya ta bayyana matsayarta kan wannan rikici.

‘Yan majalisar sun jadada bukatar  samar da zaman lafiya a yankin tare da gujewa fadawa yakin duniya na uku.

Kudurin dai ya samu goyon bayan 'yan majalisa kusan 45, waɗanda suka sama hannu gabainin a gabatar da shi gaban Majalisa.