On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Yadda Wasu Ma'aikatan Lafiya 10 Daga Jihar Kano Suka Lashe Lambobin Karramawa

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Ma'aikatan lafiya guda 10 dake aiki a asibitocin kula da lafiyar al'umma a matakin farko daban daban a Jihar Kano sun samu lambobin karramawa bisa sadaukar da kai da jajircewa.

Kungiyar matasa masu yaki da cutuka masu yaduwa YOSPIS hadin gwiwa da kungiyar HEDCODEC da tallafin  gidauniyar Aminu Magashi Garba ne suka gabatar da taron  karrama hazikan ma'aikatan lafiyan.

Shugabar kungiyar ta YOSPIS Zainab Ahmad Nasir ta ce wannan shine karo na biyu da suka gudanar da  karramawar kuma  sunyi amfani da manhajar google wajen baiwa ma'aikatan lafiyar damar neman karramawar inda kimanin mutane 78 suka nuna sha'awar shiga daga jihar  Kano da kuma birnin tarayya Abuja inda bayan tantancewa mutane 20 suka samu nassara.

Da yake tsokaci yayin taron Mallam Sulaiman Umar Jalo babban daraktan gudanarwa na gidauniyar Aminu Magashi Garba, ya ce a bara sun karrama mutane 10 a birnin tarayya Abuja, yana Mai cewa gidauniyar ta dauki gabarar tallafawa bangaren lafiya inda ta dauki Nauyin asibitoci da take basu magunguna da suka hadarda daukar maaikaciya tare da bata albashi duk wata da dai sauransu.

Ma'aikatan lafiyar da aka karrama sun bayyana lambobin  yabon amatsayin  zaburarwa garesu tareda tabbatar da cewa zasu sake zage dantse wajen ganin sunyi abun da ya dace.

Maikatan lafiyar guda 10 sun samu lambar yabo, da takardun shaida, da kuma kudi naira dubu 25 kowannensu.