Yayin da wasu matasa a Najeriya ke bata lokacinsu dake da muhimmanci wajen yin nishadi a shafukan sada zumunta, tunanin ya sha bambam ga wani matashi a hukumar Dambatta ta jihar Kano.
Sulaiman Yusuf Maitama yana amfani da kafafen sada zumunta wajen zakulo wasu kalubale domin neman ci gaba a kauyukan yankinsu wanda ke samun hadin kai daga masu ruwa da tsaki wajen magance matsalolin.
A rahoton na musamman a wannan mako tare da tallafin kungiyar Nigeria Health Watch, wakilinmu Nura Haruna Mudi, ya yi nazari kan fafutukar da Maitama ke yi tare da bukatar sauran matasa su yi koyi.
Saurari cikakken rahoton: