Da yawa-yawan maza basa damuwa da kai matansu asibiti a lokacin da suke da juna biyu, musamman a yankunan karkara na jihar Kano, Alamarin da ke haifar da karin mace macen mata masu juna biyu da kanan yara a jihar.
Wannan al’amari baya rasa nasaba da tasirin al’ada da karancin likitocin mata da ake da su dama kudin da ake kashewa ta bangaren kula da lafiya, sai kudin mota da karancin wayar da kan al’umma, wanda hakan ke cigaba da kawo babban nakasu ta bangaren haihuwa a Asibitoci.
A kan haka ne rahotonmu na musamman a wannan makon, da wakilimu Victor Chiristopher ya hada mana , yayi duba kan irin gudunmuwar da cibiyar CHRICED hadin gwiwa da wata kungiya mai rajin inganta fannin lafiya ta Health Watch ke bayarwa a wannan fannin domin ganin an samu sauyin da ake bukata.
Saurari Cikakken Rahoton.