Bankunan kasuwanci a Kano sun bayyana damuwarsu akan yadda babban bankin kasa CBN ya takaita ba su takardun kudi na Naira, inda suka bayyana cewa da yuwuwar a samu karancin takardun Kudi.
Arewa Radio ta ziyarci bankuna da dama da suka hadar da Bankin Zenith da FCMB da Access da bankin GT dake kan hanyar Murtala Muhammad, inda dukannin su suka bayyana damuwa akan al’amarin.
A sakamakon karancin samun takardun nairar, wasu bankuna sun rage adadin kudin da suke bari a cire a cikin bankin.
Sai dai wani ma’aikaci a daya daga cikin bankunan daya bukaci a sakaya sunan sa, yace abunda yake tunanin ka iya kawo wannan matsalar shine Mutane sun rage kawo ajiyar kudi a bankunan.
A yayin da bankunan suke fama da wadanan matsaloli, babu wani bayani akan dalilin takaita samar da takardun naira ga bankuna daga bangaren babban bankin kasa CBN.